- Gwamnan Zamfara ya nuna damuwa kan yadda sojoji da ƴan sanda suka sa wasa a lamarin yaƙi da ƴan bindiga a Arewa maso Yamma
- Dauda Lawal ya ce halayyar jami'an tsaron waɗanda ke karkashin gwamnatin tarayya ne ya sa shi kafa rundunar asakarawan Zamfara
- Ya ce a mako biyu za a iya kakkaɓe gaba ɗaya ƴan bindiga idan har da manufar hakan a siyasance to amma ba haka lamarin yake ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Zamfara - Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya koka kan yadda ƴan sanda da sojoji suka sanya sakaci a yaƙi da ƴan bindiga a shiyyar Arewa maso Yamma.
Gwamma Lawal ya ce halayen da jami'an tsaron gwamnatin tarayya ke nunawa ne ya jawo kirkiro rundunar ƴan sa'kai waɗanda aka fi sani da askarawan Zamfara.
Ya ce gwamnoni ba su da iko kan jami'an sojoji, ƴan sanda da jami'an tsaron fararen hula na NSCDC, wanda hakan yana kawo masu cikas a ƙoƙarin magance matsalar tsaro.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a
Dauda: "Gwamna bai da iko kan sojoji"
Da yake jawabi a cikin shirin Sunrise Daily na Channels tv ranar Talata, Gwamna Lawal ya ce:
"Mu a matsayinmu na gwamnoni, ba mu da iko a kan sojoji, ba mu da iko a kan ‘yan sanda da jami’an tsaron farin kaya, shiyasa galibi abin ke sa mu damuwa.
"Za ka ga a lokacin da muke bukatar waɗannan dakarun tsaro ba za a same su ba, bisa haka ne muka ga mafita kawai mu kafa rundunarmu ta kanmu.
Gwamna ya ce jami'an tsaro sun sa sakaci
Gwamnan ya bayyana cewa za a iya magance ƴan bindiga, waɗanda suka mayar da garkuwa da mutane sana'a, cikin makonni biyu idan aka yi niyyar hakan.
"A mako biyu za su zama tarihi amma ba a shirya hakan ba a siyasance, mun san su waye ƴan bindigar nan kuma mun san wurin da suke rayuwa."
- Dauda Lawal