Alakar kudi a matsayin kadarar musaya mai daraja ya ta'allaka da yadda al'umma ke mu'amalantarsu, a Najeriya ma, batun bai sauya zane ba.
Zai baku sha'awa da matukar burgewa ku san yadda ake hada-hada a shekarun da suka gabata a Najeriya ba tare da kudin takarda ko tsaba ko sulalla ba, da kuma yadda lamarin ya sauya zuwa yanzu.
A cikin wannan rahoton, Legit ta tattaro daga Babban Bankin Najeriya abubuwan da ake huldar cinikayya dasu kafin zuwan kudin takarda da sulalla ko tsaba da kuma yadda aka samar da kudaden da muke kashe wa yanzu.
1. A da an yi cinikayya da gishiri
Za ku ji batun kamar almara, amma gaskiya ne. A cewar Babban Bankin Najeriya (CBN), kayayyaki kamarsu gishiri, kwalba ko kayan karau da sauran abubuwa sun kasance abubuwa masu daraja a madadin kudi kafin zuwan turawan mulkin mallaka.
2. Zuwan karfe; sulalla
A farkon zuwan sulalla, Bankin Ingila ke lura da su kuma ke samar dasu a matsayin wata harkalla mai zaman kanta. Wannan ya ci gaba har zuwa shekarar 1912.
3. Zuwan kudin takarda mallakar turawa
Kamar dai sauran kasashen Afrika ta Yamma, mafi girman kudin takarda da Najeriya ta fara mallaka shi ne fam. A bangare guda, sule kuwa shi ne mafi darajan tsaba na karfe.