Yajin Aiki: Fitaccen Mawaƙin Najeriya, Falz, Ya Tafka Asarar Miliyoyin Naira a Awa 48

Yajin Aiki: Fitaccen Mawaƙin Najeriya, Falz, Ya Tafka Asarar Miliyoyin Naira a Awa 48
  • Yajin aikin kasa da awanni 48 da 'yan kwadago suka yi a Najeriya ya shafi fitaccen mawaki Folarin Falana, wanda aka fi sani da Falz
  • Falz ya ce ya yi asarar dukkanin kudin da ya kashe wajen shirya daukar wani bidiyo saboda ya gaza komawa Legas daga Uyo
  • Sai dai mawakin ya ce ya fahimci dalilan yin yajin aikin, inda ya kara da cewa yana goyon bayan bukatun kungiyoyin kwadagon

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Uyo - Fitaccen mawakin Najeriya, Folarin Falana, wanda aka fi sani da Falz, ya bayyana yadda yajin aikin da kungiyar kwadago ta yi ya sa ya yi asarar kudi masu yawa.

Kara karanta wannan

Kaduna: An shiga tashin hankali, wata amarya ta datse mazakutar angonta

Falz ya ce ya yi asarar dukkanin kudin da ya kashe wajen shirya daukar wani bidiyon wakarsa saboda ya gaza komawa Legas daga Uyo.

Mawaki ya yi asara saboda yajin-aiki

Da yake magana a wani sakon bidiyo wanda shafin Abuja Gist ya wallafa a Instagram, Falz ya bayyana cewa yajin aikin ne ya sa ya makale a garin Uyo saboda an rufe filayen jiragen sama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a

Sai dai mawakin ya ce ya fahimci dalilan gudanar da yajin aikin, inda ya kara da cewa yana goyon bayan bukatun kungiyoyin kwadago, in ji rahoton jaridar The Nation.

"Ina goyon bayan 'yan kwadago" - Falz

Falz ya ce:

“Na farka da safiyar yau, na tashi da zummar zuwa filin jirgi kawai sai na ji labarin an rufe filin jirgin, an soke dukkanin tashin jirage saboda yajin aiki.

Kara karanta wannan

Kungiyar ƙwadago ta janye yajin aiki, ta ba gwamnatin tarayya wa'adin mako 1

"Akwai bidiyon da ya kamata in yi a Legas yau amma na makale a Uyo, na yi asarar kudi masu yawa saboda mun riga mun biya kudin ajiyar wasu kaya, yanzu dole mu sake biya.
"Duk da cewa yajin aikin ya shafe ni sosai, amma na fahimci dalilin yin shi kuma ina tare da su. Ina tare da 'yan kwadago domin tuntuni ya kamata ayi hakan."
Maya Lin-Takahashi
Author

Maya Lin-Takahashi

Maya is a hardware enthusiast who tests and reviews smart home devices, smartphones, wearables, and audio gear. She focuses on practical consumer value and build quality.